Yakin man fetur

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta- OPEC Plus, watau mambobin kungiyar OPEC da Rasha sun dauki tsawon lokaci suna kokarin yadda farashin man fetur zai kasance a wani mataki na bai daya

1377954
Yakin man fetur

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta- OPEC Plus, watau mambobin kungiyar OPEC da Rasha sun dauki tsawon lokaci suna kokarin yadda farashin man fetur zai kasance a wani mataki na bai daya; ta hanyar samar da daidaito tsakanin yawan man da ake fitarwa da wanda ake bukata. Sai dai nasara akan hakan na cin tura, musanman yadda Amurka ke ci gaba da habbaka yawan man Shale da take samarwa daga duwatsu, hakan ya kara rage kiman kasuwanci da tsarin na kungiyar OPEC Plus duk da dai sun yi nasarar ci gaba da hurda a tsakaninsu. Bulluwar kwayar cutar Corona Virus wacce ta kasance babbar kalubale ga harkokin kasuwanci da ma tattalin arzikin duniya ya sanya raguwar yawan man fetur da ake bukata lamarin da ya haifar da dakatar da yarjejeniyar dake tsakanin kasashen Opec Plus game da yawan man fetur da za’a rinka fitarwa inda da jagorancin Saudiyya da Rasha suka fara gwagarmaya mai girma a tsakaninsu.

 

A wannan makon a cikin wannan maudu’in na mu mun kasance tare da manazarcin harkokin waje Mal. Can ACUN daga Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA……

 

Kwayar cutar Corona Virus da ta bulla a garin Wuham dake kasar China, baya ga kasancewa babban kalubale ga harkokin kiwon lafiya; ta kuma kasance cutar da ke nakasar da tattalin arziki a doron kasa. A yayinda sarrafa da kera kayayyaki ya ragu kwaran gaske a China da ma a kasashen da suka bunkasa, kashe kudaden wadanda aka kebe sanadiyar cutar ya karanta. Cikin wanann halin ne kuma yawan man fetur da duniya ke bukata ya fara raguwa. Ganin hakan ne ya sanya Asusun IMF, bankuna da sauran hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa suka fara sharhin cewa ga dukkan alamu duniya za ta fuskanci tabarbarewar tattalin arziki. Hakan ya sanya ake kuma hasashen cewa bukatar man fetur a doron kasa zai ragu kwaran gaske a cikin wannan shekarar ta 2020. Dangane ga hasashen Hukumar Makamashi ta Duniya, yawan man da ake bukata a duniya a ko wace rana zai ragu akallan da ganga miliyan 3 zuwa 4.

 

A yayinda ake hangen cewa yawan man fetur da ake bukata a duniya zai ci gaba da raguwa, Amurka ke ta kokarin kara yawan man Shale da take samarwa daga duwatsu. A halin yanzu dai Amurka ta fara iya samarda man fetur har ganga miliyan 12-13 a rana. Sakamakon bunkasar kimiyya da fasaha a yau ana ci gaba da samun nasarar raguwar kudaden da ake kashewa wajen samar da irin wannan man fetur din daga duwatsu. Wannan tsarin dai ya bar kasashen masu man fetur din gargajiya da suka hada da Saudiyya da Rasha cikin zullumi mai girma.

 

Saudiyya dai na bukatar a ci gaba da mutunta yarjejeniyar Opec plus inda take neman ma a kara rage yawan man da ake fitarwa da ganaga miliyan 1.5a rana, amma Rasha bata da bukatar hakan domin ganin cewa hakan zai inganta lamurkan abokan hamayarsu kaman Amurka ya kuma sanya su samun nakasu a kasuwar mai ta duniya. Lamurka tsakanin kasashe masu albarkatun mai ya gurbace bayan rashin cimma matsaya da ba’a yi ba a taron kolin Vienna. Domin Saudiyya da Rasha sun zabi su kara yawan gangunan man da suke fitarwa a ko wacce rana da zummar karin samun rabo a kasuwar man ta kasa da kasa. Hakan ne dai ya sanya faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya warwas da ragin kusan kaso 30 cikin dari. Dangane ga hasashen masana harkokin mai, sun bayyana cewa farashin gangar man zai iya faduwa zuwa dalar Amurka 20. Idan wannan farashin ya kasance zai jefa kasashe masu man fetur musanman wadanda tattalin arzikinsu ya dogara gareshi cikin tabarbarewar tattalin arziki da mawuyacin hali.

 

Wannan sharhin Mal. Can ACUN ne daga Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya……Labarai masu alaka