A yayinda lokacin da Turkiyya ta baiwa gwamnatin Siriya ke karewa a Idlib....

Masifu na ci gaba da dada karuwa ga al’umman Idlib. A cikin wata dayan daya gabata kawai fiye mutum miliyan daya suka tattara nasu-inasu suka fice daga yankin

1368836
A yayinda lokacin da Turkiyya ta baiwa gwamnatin Siriya ke karewa a Idlib....

Masifu na ci gaba da dada karuwa ga al’umman Idlib. A cikin wata dayan daya gabata kawai fiye mutum miliyan daya suka tattara nasu-inasu suka fice daga yankin. Gwamnatin kasar da dakarun Shi’a na ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta kasa a yankunan. Ba wai akan sojojin dake adawa da gwamnatin kasar kawai ba; har ma ga fararen hula. Ita kuwa Turkiyya na ci gaba da daukar matakan siyasa dama na soja domin kawo karshen rikicin na Idlib.  Lokacin da shugaba Erdogan ya baiwa gwamnatin Asad na su dakatar da hare-haren da suka kaiwa a yankin ya kusan kawo karshe. Ana dai ganin a yayinda Turkiyya ke ci gaba da daukar matakan siyasa inda take tattaunawa da Rasha akan lamarin, ana kuma ganin cewa zata iya daukar matakan soja idan har dalilin hakan ya taso.

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Mal.  Can ACUN daga Gidauniyar SETA…..

 

Rikici na ci gaba da afkuwa a yankunan Idlib biyu. Yanki na farko dai shi ne yankin Neyrab-Serakip. Akwai muhimman guraren zama a wannan yankin da hanyoyin m4 da m5 suka hada. A ‘yan kwanakin da suka gabata dakarun gwamnatin kasar da goyon bayan  Rasha sun yi nasarar karbe ikon wannan yankin bayan kai hare-hare ta sama. A dayan barayin kuma da taimakon sojojin Turkiyya dakarun dake adawa da gwamnatin kasar sun yi nasarar sake karbe ikon yankin Neyrab daga hannun dakarun gwamnatin. Daga bisani kuma sunka kutsa zuwa cikin yankin na Serakib. Akwai rahotannin dake nuna cewa dakarun gwamnatin kasar Siriya da kungiyoyin Shi’a sun yi asara mai yawa, lamarin dake jaddada ingancin salon yakin sojojin Turkiyya da kuma muhinmancin daukar nauyin dakarunta da take da kyau.

 

Sashi na biyu kuma da ake gwabza rikici akai shi ne yankin Cebetül Zaviye da a cikinsa ne kudancin Idlib yake. An dai ga cewa dakarun gwamnatin Siriya sun yi yunkurin afkawa wannan yankin daga arewa ta titin m4.   Lamarin da yasa aka fara tura sojojin Turkiyya wannan yankin domin taimakawa dakarun dake adawa da gwamnatin ta Siriya, sabili da haka duk da dai dakarun gwamnatin sun yi nasarar karbe ikon wasu kauyuka har yanzu basu iya kaiwa ga yankin ba.

A yayinda ake ta jan daga a fili, ana kuma ci gaba da zama akan teburin samar da zaman lafiya a yankin. Domin a dai-dai lokacin da Turkiyya ke tattaunawa da Rasha, tana kuma neman kungiyoyin kasa da kasa  da masu fada aji domin su dauki mataki akan matsalar Idlib. Musamman yadda take neman Amurka da kasashen Nahiyar Turai da su dauki matakan diflomasiyar kalubalantar matakan Rasha da Iran a yankin Idlib.

 

Ana dai ganin cewa Amurka da kasashen Turai na goyon bayan matakan da Turkiyya ke dauka a yankin na Idlib. A yayinda Turai ke fargaban matsalar Idlib ka iya haifar da kwararar ‘yan gudun hijira, ita kuwa Amurka bata bukatar Rasha  da Iran su yi nasara a kasar Siriya. Anan dai akwai bukatar a yi babar tamabaya, shin ko Amurka tana goyawa Turkiyya baya ne da wata manufa ko kuwa tana yi ne domin a magance matsalolin Idlib? Idan dai har Amurka tana neman kare muradunta ne a yankin Idlib ya kamata ya kuma zama wajibi ta dauki kwararan matakai na zahiri.

Wannan sharhin Mal. Can ACUN ne daga Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da kuma Halayyar dan Adam watau SETA
 Labarai masu alaka