Namiji mafi tsufa a duniya ya mutu

An sanar da mutuwar Chitetsu Watanabe mutumin da Guinness Book of record ta bayyana a matsayin manikin da ya fi tsufa a duniya ya mutu yana da shekaru 112

1365887
Namiji mafi tsufa a duniya ya mutu

An sanar da mutuwar Chitetsu Watanabe mutumin da Guinness Book of record ta bayyana a matsayin manikin da ya fi tsufa a duniya ya mutu yana da shekaru 112.

Mutumin dake zaune a wani gidan kula da tsaffi a yankin Niigata dake kasar Japan a ranar 12 ga watan Febrairu ne Hukumar Guinness ta bashi satifiket din cewa shu ne namijin da ya fi tsofa a duniya. An haifi Chitetsu Watanabe ne a ranar 5 ga watan Maris din shekarar 1907 ya kuma rasu a yayinda yake kusa da cika shekaru 113.

Hukumomi sun tabbatar da cewa, Watanabe ya rasu ne a ranar 23 ga watan Febrairu ranar Lahadi.

Jaridar Mainichi ta kasar Japan ta bayyana cewar dangin Watanabe ya kasance yana fama da zazzabi da kuma rashin cin abinci a cikin yan kwanaki gabanin rasuwarsa.

Labarin ya kara da cewa Watanabe wanda ya ksance namıjı mafı tsofa a dunıya ya mutu yabar yara 5, jikoki 12, tattaba kunne 16 da kuma tankada haude 1.

A lokacin da yake raye an tambayi Watanabe sirrin samun yawan shekaru inda ya bayar da amsa da cewa "Rashin bacin rai da kuma yawan murmushi".

A watan Janairun 2019 da Masazo Nonaka dake yankin Hokkaido a kasar Japan mai shekaru 113 ya rasu ne aka bayyana Watanabe a matsayin namiji mafi tsufa a duniya. 

A watan Maris din shekarar 2019 ne hukumar Guinness ta bayyana wata mata yar kasar Japan mai suna Kane Tanaka mai shekaru 116 a matsayar wacce ya fi kowa tsufa a duniya. 

Tanaka wacce ta yi bukin cikanta shekaru 117 a watan jiya ta kasance wacce ta fi kowa tsufa a duniya ne bayan rasuwar Chiyo Miyako tana da shekaru 117 a watan Yuli 2918.

Dangane ga kundin tarihin Guinness Book of Record bil adaman da ya fi dadewa a duniya wata mata ce yar kasar Faransa mai suna Louise Calment wacce ta rasu tana da shekaru 122 a shekarar 1997.

 

 

 

 Labarai masu alaka