MDD ta kara wa'adin takunkumin sayen makamai da ta kakaba wa Yaman

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar ya kara wa'adin shekara daya na takunkumin sayen makamai da ya kakaba wa kasar Yaman.

1366593

Bayan da Rasha da China suka ki jefa kuri'a ne aka amince da kudirin da Ingila ta gabatar na neman a kara wa'adin takunkumin sayen makamai da aka kakaba wa Yaman.

Barazanar karfin ikon da Rasha ta ke da ita a Majalisar ba ta yi aiki ba game da makaman da ake zargin mayakan Houthi suna samu daga Iran.

An kara wa'adin takunumin ga Yaman har nan da watan Fabrairun shekarar 2021.Labarai masu alaka