Corona ta bulla a kasar Oman

Gwamnatin Oman ta sanar da cewar an samu wasu 'yan kasarta 2 dauke da cutar Corona bayan sun dawo daga Iran.

1365687
Corona ta bulla a kasar Oman

Gwamnatin Oman ta sanar da cewar an samu wasu 'yan kasarta 2 dauke da cutar Corona bayan sun dawo daga Iran.

Ma'aikatar Lafiya ta Oman ce ta sanar da hakan inda ta ce mutanen 2 da aka samu daule da cutar corona (Convid-19) sun dawo kasar daga Iran.

Sanarwar da Ma'aikatar Lafiyar ta fitar ta gidan talabijin din kasa na Oman ta ce, an killace mutanen 2 kuma ba sa cikin mummunan yanayi.

Sanarwar ta ce wannan ne karon farko da cutar ta Convid-19 ta bulla a kasar.

Hukumar Kula da Sifirin Jiragen sama ta Oman ta ce an dakatar a zirga-zirga tsakanin kasar da Iran.

Ya zuwa yanzu mutane 14 ne aka sanar da sun mutu sakamakon kamuwa da cutar corona a Iran. Cutar ta kama jimillar mutane 47 a kasar.

A baya ma an samu bullar cutar corona a kasashen Gulf da suka hada da Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrayn.Labarai masu alaka