An kashe mutane 4 a harin 'yan bindiga a Iraki

Mutane 4 da suka hada da jami'an tsaro ne suka rasa rayukansu, wasu 6 kuma suka jikkata sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a yankunan Bagdad da Diyala dake kasar Iraki.

Sanarwar da aka fitar daga ofishin 'yan sandan Bagdat ta ce a harin da aka kai a yankin Betul na gabashin birnin an kashe wani dan sandan kula da hanya, a yankin Nasr kuma an kashe fararen hula 1 sakamakon wani harin na daban da aka kai.

A yankin Sadr na gabashin babban birnin Irakin an kai hari a kan babur tare da kashe wani jami'in Ma'aikatar Ilimi guda 1.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta fitar ta ce an kashe farar hula 1 a harin da aka kai a jihar Diyala dake gabashin Bagdad, a hari kan shingen bincike ababan hawa da kungiyar ta'adda ta Daesh ta kai an jikkata 'yan sanda 3.

Tag: Iraki

Labarai masu alaka