A karon farko corona ta bulla a Bahrayn

Ma'aikatar Lafiya ta Bahrayn ta bayyana cewar a karon farko an samu bullar cutar corona a kasar bayan da wani dan kasar ya dawo daga Iran.

A karon farko corona ta bulla a Bahrayn

Ma'aikatar Lafiya ta Bahrayn ta bayyana cewar a karon farko an samu bullar cutar corona a kasar bayan da wani dan kasar ya dawo daga Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Bahrayn BNA ya fadi cewar an kai mutumin da ya dawo daga Iran zuwa asibitin Ibrahim Khalin Kanun dake yankin Selmaniye.

An bayyana cewar bayan gwaje-gwaje an samu alamun cutar a tare da mutumin.

Rubutacciyar sanarwar Ma'aikatar Lafiya ta ce wannan ne karo na farko da aka samu bullar cutar a kasar ta Bahrayn.

 Labarai masu alaka