Erdoğan ya yi kira da a hada kai domin magance rikicin Siriya

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a tattaunawarsa da takwarorinsa na Faransa Emmanuel Macron da Chancellor Jamus Angela Merkel ta wayar tarho sun tabo batun harin da ‘yan ta’adda masu tsattsaurar ra’ayi suka kai Hanau din Jamus

Erdoğan ya yi kira da a hada kai domin magance rikicin Siriya

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a tattaunawarsa da takwarorinsa na Faransa Emmanuel Macron da Chancellor Jamus Angela Merkel ta wayar tarho sun tabo batun harin da ‘yan ta’adda masu tsattsaurar ra’ayi suka kai Hanau din Jamus da kuma rikice-rikicen da ake fama dasu a Idlib  din Siriya da kuma Libiya.

Erdoğan ya mika sakon ta’aziyya akan wadanda suka rasa rayukansu a harin nuna wariyar launin fatar da aka kai a Hanau inda kuma ya yi Allah wadai da ire-iren harin da ake kaiwa domin kyamar baki da kyamar Islama.

Jakadan Turkiyya a Jamus Ali Kemal Aydin ya bayyana cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a harin na Hanau akwai Turkawa biyar.

Akan lamarin Siriya kuwa shugaba Erdoğan ya bayyana cewa ya kamata a dakatar da irin cin zarafin da gwamnatin Bashar Assad ke ayyanarwa a kasar. Ya kara da cewa akwai bukatar a hada kai domin magance rikice-rikicen dake addabar kasashen Siriya da Libiya.Labarai masu alaka