Coronavirus: Rasha da Amurka na zargin juna

Jaridar Daily Sabah ta kasar Turkiyya ta rawaito cewa wani jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa dubun-dubatan kafafen sadar da zumunta da aka ta’alaka da Rasha na yada bayanan dake tayar da hankula game da Corona Virus lamarin da zai iya zama kalubale

Coronavirus: Rasha da Amurka na zargin juna

Jaridar Daily Sabah ta kasar Turkiyya ta rawaito cewa wani jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa dubun-dubatan kafafen sadar da zumunta da aka ta’alaka da Rasha na yada bayanan dake tayar da hankula game da Corona Virus lamarin da zai iya zama kalubale ga yakar kwayar cutar.

Kanfen din da bai da tushe ana yinsu ne da zummar bayyana cewa Amurka ce ta yi sanadiyar kwayar cutar ta COVID-19 domin bata mata suna a idon duniya.

Hukumar dake da alhakin karyata farfagandar Rasha ta shaidawa kanfanin dillancin labaran France -Press (AFP) da cewa ana amfani da kafafen sadar da zumuntar Twitter, Facebook da Instagram na karya domin yada farfagandar Rasha ta harsuna daban-daban.

Mataimakin sakataren harkokin waje na Amurka mai kula da yankunan Turai da Asiya Philip Reeker ya bayyana cewa babban manufar Rasha dai ita ce ta batawa ma’aikatun Amurka suna ta hanyar kanfen din da basu da kan gado.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai aka fara ikirarin cewa Amurka ce ta kirkiri corona virus domin ci gaba da kara gwabin yakin kasuwancin da take yi da China. Inda ake kuma bayyana cewa hukumar leken asirin Amurka ta CIA ce ta kirkiri corona virus a matsayin makamin ilimin halitta domin kalubalanatar  kasar ta China.

 Labarai masu alaka