Tilastawa gwamantin Siriya da kawayenta zuwa ga tsarin zaman lafiya a Idlib

Sojojin gwamnatin Asad na ci gaba da sabawa yarjejeniyar Astana ta kai hare-hare a Idlib sabili da gudumowar da suke ci gaba da samu daga Rasha da Iran

1359867
Tilastawa gwamantin Siriya da kawayenta zuwa ga tsarin zaman lafiya a Idlib

Sojojin gwamnatin Asad na ci gaba da sabawa yarjejeniyar Astana ta kai hare-hare a Idlib sabili da gudumowar da suke ci gaba da samu daga Rasha da Iran. A yayinda dakarun gwamnatin ke ci gaba da mallake yankunan M4-M5 da kuma yankunan Serakib zuwa El Eys, a cikin shekarar data gabata sun yi dalilin yin kaurar fiye da mutane miliyan daya da rabi daga matsugunansu. A yayinda gwamnatin kasar da kawayenta ke daukar matakan soja da kuma watsi da hanyoyin lumana domin kawo karshen matsalar Idlib, Turkiyya na ci gaba da daukar matakan kalubalantar wadannan matakan nasu da ba zata iya bayar da izini akansu ba.

Akan wannan mauduin mun kasancewa tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA

A cikin makonni biyu da suka gabata dakarun gwamnatin Siriya sun yawaita hare-haren da suke kaiwa a yankunan ldlib, a daidai wannan lokacin kuma kungiyoyin Shi’a dake da alaka da lran sunka kara yawan hare-haren da suke kaiwa ta kasa, Rasha kuma ta sama, lamarin daya kara wa dakarun gwamnatin karfin gwiwar kalubalantar ‘yan adawar kasar. Bayan sun yi nasarar karbe ikon gari mafi girma a yankin ldlib watau Maaret el Numan, suka kuma karbe ikon garin Serakib inda hanyoyin M4-M5 suke.

A dalilin haka dubun dubatan fararen hula suka fara yin hijira zuwa Turkiyya domin kauracewa yankunan da ake yawan bude musu wuta. Ganin hakan ya sanya Turkiyya daukar matakai na fadakarwa ta soja domin kalubalantar yunkurin dakarun gwamnatin Siriya. Sabili da hare haren da dakarun gwamnatin Siriya suka kai a sansanonin sojojin Turkiyya dake yankunan Serakib da Teftanaz, suka sanya Turkiyya daukar matakan kalubalantar sojojin Siriya karon farko tun bayan barkewar yakin basasar kasar. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ma ya ja kunne da cewa idan har dakarun gwamnatin Siriya basu fice daga yankunan lumana da aka bayyanar a lokacin yarjejeniyar Sochi ba, a karshen watan Febrairu Turkiyya zata dauki matakan soja domin kaudasu daga yankunan.

Kalaman shugaba Erdogan dai na nuni da cewa sojojin Turkiyya zasu kara gwabin da suke dashi a yankunan ldlib, lamarin da zai haifar da wata tsarin dangantaka a yankunan baki daya. Turkiyya na ci gaba da neman a mutunta yarjejeniyar Sochi da aka yi da Rasha, sabili da haka dakarun kasar Siriya ya kamata su fice daga yankunan lumana, sai dai wannan lamari mai kamar wuya. Ana dai ganin cewa Turkiyya da masu adawa da gwamnatin Siriya zasu sauya da karfafa yankunan sa idonsu 12 a yankunan su fara daukar matakan soja a yankunan.

Baya ga matakan da gwamnatin kasar ke dauka, matakan da Rasha ta fara dauka a cikin ‘yan kwanakin nan basu kasance ba face cutarwa ga Turkiyya. Lokaci dai ya yi da Rasha zata fahimci muhinmancin dangantaka da kawarta Turkiyya . A karshe dai ya kamata Turkiyyya ta yi la’akari da cewa daukar matakan soja zai haifar mata da kashe kudade ta kuma dubi muhimancin samar da lumana, tamkar haka ne kuma ya kamata Rasha ta amince da matakan samar da lumana a yankin bisa tsarin diflomasiyya.

Wannan sharhin Mal Can ACUN ne mai binciken harkokin waje a Gidauniyar SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.

 

                                          Labarai masu alaka