Dutsen Merapi na Indonesiya ya dawo da yin aman wuta

Dutsen Merapi dake Tsibirin Java na Kasar Indonesiya ya yi wata bindiga mai karfi tare da dawo da aman wuta.

Dutsen Merapi na Indonesiya ya dawo da yin aman wuta

Dutsen Merapi dake Tsibirin Java na Kasar Indonesiya ya yi wata bindiga mai karfi tare da dawo da aman wuta.

Labaran da jaridar Tempo ta fitar na cewa dutsen na Merapi dake garin Yogyakarta ya yi bindiga da misalin karfe 05.15 na Asubahin ranar Alhamis din nan.

Mahukunta sun ce bakin hayaki da tokar da dutsen ke fitarwa sun kai nisan mita dubu 2 a sama.

Hukumar Kula da Duwatsu Masu Aman Wuta ta Indonesiya ta gargadi mutane da kar su kusanci dutsen da nisan kilomita 3.

A shekarar 2010 ma dutsen na Merapi ya yi aman wutar da ta yi ajalin mutane 347 a yankin.Labarai masu alaka