An yi barazanar kaiwa Masallatai uku harin bam a Jamus

A wasu masallatai uku dake biranen Essen, Hagen da Unna a jihar arewcin Ren Vestfalya a kasar Jamus an yi gargadi mara tushe da cewa akwai yiwuwa an ajiye bama-bamai a cikinsu

An yi barazanar kaiwa Masallatai uku harin bam a Jamus

A wasu masallatai uku dake biranen Essen, Hagen da Unna a jihar arewcin Ren Vestfalya a kasar Jamus an yi gargadi mara tushe da cewa akwai yiwuwa an ajiye bama-bamai a cikinsu.

Hukumar Haddin Kan Turkawa Musulmi (DİTİB) ta sanar da hukumar 'yan sanda wasikar da ta samu  ta yanar gizo wanda aka yi ikirari da barazanar cewa "Zamu wargaza masallatai a iska"

Jami'an 'yan sanda sun nemi a kauracewa masallatan inda suka gudanar da bincike tare da masana da karnukan masu gano bama-bamai a cikin masallatan.

Hukumar 'yan sandan Essen ta yada a kafarta ta Twitter da cewa a binciken da suka gudanar a masallatan ba'a samu wani bam ba sabili da haka barazanar bata da tushe ko kan gado.

Tuni dai hukumar 'yan sandan yankunan sun bayar da damar a ci gaba da hada-hada kamar yadda aka saba.

 Labarai masu alaka