Sharhi akan ibtila'in al'umman Idlib

Da taimakon Rasha da Iran gwamnatin Asad ta dauki tsawon lokaci tana kai hare-hare a yankin Idlib. A cikin shekaru biyu da suka gabata kachal; mutane fiye da dubu 200 sun tilastu da yin hijira daga matsugunansu dubun-dubata kuma sun rasa rayukansu

Sharhi akan ibtila'in al'umman Idlib

Da taimakon Rasha da Iran gwamnatin Asad ta dauki tsawon lokaci tana kai hare-hare a yankin Idlib. A cikin shekaru biyu da suka gabata kachal; mutane fiye da dubu 200 sun tilastu da yin hijira daga matsugunansu a yayinda kuma dubun-dubata suka rasa rayukansu ko kuma suka raunana. Gwamnatin kasar da kawayenta basu kasance masu kaiwa sansanin sojoji hari kawai ba, har ma da yankunan fararen hula. Tsarinsu dai shi ne su kauda al’umma ko ta wace hanya gabanin su mallake yankunan da suke bukata. Yankin Idlib wanda ya kasance gurin da ya ragewa ‘yan adawan kasar kawai, gwamnatin kasar na ci gaba da daukar miyagun matakan da ke haifar da ficewar mafi yawan al’umman daka yankin mai mazauna miliyon hudu. A cikin wanann yanayin ne dai Turkiyya ta kasance kasar dake daukar dukkanin matakan da suka dace domin kare dukkanin bala’o’in da al’umman yankin ke fuskanta.

 

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Malam Can ACUN manazarcin harkokin kasashen waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA..

 

Duk da yaryejeniyar Sochi da aka gudanar a watan Satumbar shekarar 2018 gwamnatin Asad na ci gaba da kai hare-hare a yankin Idlib. Haka kuma bayan kaddamar da hare-hare ta sama da Rasha ta yi ya kara jefa yankin cikin halin kakanikayi. Hare-haren da gwamnatin kasar ta fara a watan Afirilun shekarar 2019 ya sanya ta samu nasarar karbe wasu yankunan arewacin Hama, haka kuma lamarin ya sanya matsewa yankin da sansanin sojojin Turkiyya ya ke a Morek, daga karshe kuma ya haifar da karbe ikon yankin Han Sheyhun da ya kasance hannun ‘yan adawan kasar ta Siriya.

 

A cikin wannan lokacin da kuma hare-hare da aka dinga kaiwa yankin da ma hare-haren da Rasha ta rinka kaiwa ta sama ya sanya dubun-dubata mutane yin hijira daga matsugunansu. An bayyana cewa a gundumar Idlib mutane miliyan daya da dubu dari shidda suka yi kaura daga yankunansu sanadiyar yawan hare-haren da aka dinga kaiwa a yankin. Haka kuma hare-haren sun yi sanadiyar hasarar dukiyoyin da kadarinsu ya kai na dala miliyan 322. A cikin ‘yan kwanakin nan ma hare-haren sai da ya kusan shafar sansanin da sojojin Turkiyya ke sa ido dake yankin Surman.

 

A hare-haren da aka fara a watan Disambar shekarar 2019 kuwa, ya haifar da da yin hijirar mutane dubu 400 daga yankin inda suka nemi mafaka a Turkiyya. Sanadiyar hare-haren da gwamnatin Asad ta fara kaiwa a cikin ‘yan kwanakin nan a yankunan kudu masu gabashin Idlib da yammacin Halep ya basu damar karbe ikon titin M5, da kuma ma yankin garin Maarat al Numan. Ana hasashen dai da karbe ikon titunan M4 da M5, Rasha da gwamnatin Asad zusu iya fara kai hare-haren bama-bamai ta kasa domin karbe ikon garin Idlib.

 

Dukkan wadannan tabi’un hare-haren a Idlib basu kasance komai ba face yunkurin da gwamnatin Asad, Iran da Rasha suke yi na kauda farar hula daga yankin, tilasta musu yin hijira zuwa wasu kasashen domin su samu  damar iya mülkin yankin kamar yada suke so. A bisa wanan bukatar suna iya daukar ko wani irin matakin da zasu kori mutane ko ma hallakasu a yankin. Haka kuma ana iya sharhin cewa ana kaiwa yankin Idlib hare-hare ne domin kasancewar yankin mazaunar masu adawa da gwamnatin kasar ne kuma yanki ne wanda keda kungiyoyi masu dauke da miyagun makamai.  Turkiyya ta kasance tana kalubalantar gwamnatin Asad da kawayenta domin samawa al’umman Idlib zaman lafiya, ko dai don akallan ta rage masifun dake yankin. A dayan barayin kuma, Turkiyya na daukar matakan siyasa da diflomasiyya tare da Rasha da kuma kokarin hada kawunan hukumomin kasa da kasa domin samar da mafita ga matsalolin dake addabar yankin na Idlib. Sai dai duk da haka, hukumomin kasa da kasa na ci gaba da juyawa  miliyoyin al’umman Idlib baya domin sun kasa daukar matakan da suka dace a yankin.

 

Wannan sharhin Malam Can ACUN manazarcin harkokin kasashen waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.Labarai masu alaka