Manyan ‘yan siyasa Musulmai sun fice daga jam’iyyar dake mulkin lndiya

Sanadiyar bakadalar sauya dokar zama dan kasa dake nuna wariya ga Musulman lndiya jigajigan siyasa Musulmai 80 sun fita daga jamiyyar BJP dake mulkin kasar lndiya

Manyan ‘yan siyasa Musulmai sun fice daga jam’iyyar dake mulkin lndiya

Sanadiyar bakadalar sauya dokar zama dan kasa dake nuna wariya ga Musulman lndiya jigajigan  siyasa Musulmai  80 sun fita daga jamiyyar BJP dake mulkin kasar lndiya.

Dangane da labaran da kafafen yada Labaran cikin gidan lndiya suka rawaito domin kalubalantar tsarin zama dan kasa da gwamnati ke yi wanda zai zama kalubale ga Musulmi wasu manyan yan siyasa Musulmi su 80 sun sauya sheka daga jamiyyar dake kan karagar mulki a kasar.

Wadanda suka fice daga jamiyyar sun bayyana yin hakan domin nuna kyama ga tsarin zama dan kasa da aka fitar dake nuna wariyar addini.

A makon jiya ma musulmai yan siyasa 50 suka fita daga jamiyyar ta BJP.

A dokar dai an amince a baiwa wadanda ba Musulmi ba da suka shiga kasar lndiya bayan 31 ga watan Disambar shekarar 2014 shaidan zama dan kasa, amma dokar ba ya yarda da a baiwa Musulmai dake cikin irin yanayin ba shaidar zama dan kasar.

 

 Labarai masu alaka