"Makamin S-400 ya yi dai-dai da tsarin NATO"

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewa makamin S-400 da Turkiyya ta saya daga Rasha ya yi daidai da tsarin kungiyar NATO

"Makamin S-400 ya yi dai-dai da tsarin NATO"

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewa makamin S-400 da Turkiyya ta saya daga Rasha ya yi daidai da tsarin kungiyar NATO.

A yayin da yake jawabi a taron Davos minista Cavusoglu ya bayyana cewa ko wace mambar NATO ta nadan ata korafi, muma muna da namu korafin korafinmu shi ne a yayin da muke yaki da ta’addanci kawayenmu basu kawo muna dauki ba.

Haka kuma ya kara da cewa Turkiyya ta sayi makamin S-400 daga Rasha saboda bukatar hakan ta taso, mun bukaci wadannan makaman da kawayenmu da suka hada har da Amurka amma babu wanda ya bamu. Wasu na shakkun cewa ko S-400 ya yi daidai da tsarin NATO, wannan ko shakka babu wannan makamain dai-dai yake da tsarin kungiyar NATO. Wannan ba makami ne da za’a kalubalanci wata mambar NATO dashi ba.Labarai masu alaka