Amurka ta bayyana sabbin takunkuman da za ta kakkabawa Iran

Ma'aikatar kudin kasar Amurka ya fitar da wasu sabbin takunkuman tattalin arzikin da za ta kara kakkabawa lran

Amurka ta bayyana sabbin takunkuman da za ta kakkabawa Iran

Ma'aikatar kudin kasar Amurka ta fitar da wasu sabbin takunkuman tattalin arzikin da za ta kara kakkabawa domın kalubalanatar lran.

Takunkuman zasu shafi mutane biyu da kuma kanfuna shida.

An fitar da jerin sabbin takunkuman a shafin yanar gizon ma'aikatar kudin Amurka.

Hudu daga cikin kanfunan nada alaka da hukumar mai ta kasar lran.

Sanarwar ta kara da cewa an kakkaba takunkuman ne domin hukunta kanfunan dake taimakawa petrochemical da kanfunan man fetur din kasar lran.

Sanarwar kuma ta kara da cewa kanfunan petrochemical da na man fetur kasar lran dake taimakawa ta'addanci a doron kasa.

 Labarai masu alaka