An kai hari da makami mai linzami a Bagdad

An kai hari da makami mai linzami a yanki na musamman da Ma'aikatun Gwamnati suke a Bagdad Babban Birnin Iraki.

An kai hari da makami mai linzami a Bagdad

An kai hari da makami mai linzami a yanki na musamman da Ma'aikatun Gwamnati suke a Bagdad Babban Birnin Iraki.

Kafar yada labarai ta gwamnatin Iraki ta bayyana cewar makamai masu linzami guda 3 samfurin Katyusha sun fado a yankin.

Sanarwar ta ce babu wanda ya mutu ko jikkata sakamakon harin.

A baya ma an kai hare-hare da makamai masu linzami samfurin Katyusha a yankin da ofishin jakadancin Amurka yake.

 Labarai masu alaka