Gobara ta yi sanadiyar rayuka 11 a Rasha

An sanar da cewa sanadiyar gobarar da ta kama wani gida dake yankin Tumen a kasar Rasha mutane 11 sun rasa rayukansu

Gobara ta yi sanadiyar rayuka 11 a Rasha

An sanar da cewa sanadiyar gobarar da ta kama wani gida dake yankin Tumen a kasar Rasha mutane 11 sun rasa rayukansu.

Kanfanin dillancin labaran kasar Rasha watau TASS ta rawaito daga Hukumar Bayar Agajin Gaggawar kasar da cewa a tsakiyan dare wuta ta kama wani gidan da ma'aikatan gandun daji ke zama dake kauyen Prichulimskiy a yankin Tumen.

Kawo yanzu dai ba'a gano musabbabin gobarar ba amma an sanar da cewa mutane 11 da suka hada da 'yan kasar Uzbekistan sun rigamu gidan gaskiya.

Tuni dai jami'an tsaron sun soma gudanar da bincike akan lamarin.

 Labarai masu alaka