An kashe 'yan sanda 2 a Afganistan

Wasu 'yan sanda 2 da aka kai wa hari a jihar Uruzgan din Afganistan sun rasa rayukansu.

An kashe 'yan sanda 2 a Afganistan

Wasu 'yan sanda 2 da aka kai wa hari a jihar Uruzgan din Afganistan sun rasa rayukansu.

Kakakin Fadar Gwamnan uruzgan, Zilger Ibadi ya shaida cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai harin kan jami'an tsaron dake wani shingen binciken ababan hawa a yankin Mirveyis Nike na jihar.

Ya ce 'yan sanda 2 sun mutu kuma maharan sun gudu daga yankin.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.Labarai masu alaka