Putin ya tattauna da Merkel akan Libiya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya tattauna da firaministan Jamus Angela Merkel akan shirin da ake yi na gudanar da taro a Berlin akan lamurkan kasar Libiya

Putin ya tattauna da Merkel akan Libiya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya tattauna da firaministan Jamus Angela Merkel akan shirin da ake yi na gudanar da taro a Berlin akan lamurkan kasar Libiya.

Dangane da sanarwar da aka fitar a rubuce daga fadar Creamea an bayyana cewa Putin ya tattauna da Merkel ta wayar tarho.

Sanarwar ta kara da cewa a tattaunawar an tabo rikicin da Libiya ke fama dashi.

Haka kuma a tattaunawar da shugabanin biyu suka yi an aminta akan fara shirye-shiryen taron da za'a gudanar a Berlin domin kawo karshen rikicin kasar Libiya. Putin ya sanar da Merkel abubuwan da aka tattauna da bangarori daban-daban daga Libiya a taron da aka gudanar a Moscow kwanakin baya.

 

 

 Labarai masu alaka