An kashe mutane 2 a harin bam a Afganistan

Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka a garin Mezarissharif dake jihar Belh ta kasar Afganistan.

An kashe mutane 2 a harin bam a Afganistan

Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka a garin Mezarissharif dake jihar Belh ta kasar Afganistan.

Kakakin 'yan sandan Belh Adilshaf Adil ya bayyana cewar an binne bam din a gefen hanya wanda ya fashe a lokacinda jama'a suke wucewa.

Adil ya ce mutane 2 sun mutu, wasu 9 kuma sun jikkata sakamakon harin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar an tayar da bam din a gaban gidan Sakataren Gundumar Belh mai suna Gulbaz Han.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.Labarai masu alaka