An kai hari a wani Masallaci a Bosnia

An kai hari tare da fasa gilasai da rush wani sashen bangon Masallacin dake birnin Bosanska Dubica a Bosnia

An kai hari a wani Masallaci a Bosnia

An kai hari tare da fasa gilasai da rushe wani sashen bangon Masallacin dake birnin Bosanska Dubica a Bosnia.
Masallacin da anka  gina a garin Bosanska Dubica a karni na 17 an rushe shi a lokacin yakin Bosnia anka kuma sake gina shi a shekarar 2003.

Musluman Bosnia sun nuna bacin ransu akan harin da aka kaiwa Masallacin.

Babban limamin garin mai Musulmi kusan dubu biyu Safet Beganovic, ya sanar da cewa baya ga barnar da aka a cikin Masallacin an kuma lalata guraren zama dake gaban Masallacin, inda ya kara da cewa ya sanar da hukuma afkuwar lamarin.

Kugiyar Haddin Kan Musulmi a Bosnia ta fitar da sanarwa inda ta tunatar da cewa a bara ma an kaiwa Masallacin irin wannan harin.

Magajin garin birnin Radenko Reljic ya yi Allah wadai da harin da aka kai ya yi kuma alkawarin daukar nauyin gyara Masallacin.

 Labarai masu alaka