Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 11 a Afganistan

Mutane 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihohin Kandahar da Helmand din kudancin Afganistan.

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 11 a Afganistan

Mutane 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihohin Kandahar da Helmand din kudancin Afganistan.

Fadar Gwamnan Kandahar ta bayyana cewar sakamakon mamakon ruwan sama da ake ci gaba da yi mutane 8 sun mutu yayinda wasu 14 suka jikkata.

Fadar Gwamnan Helmand kuma cewa ta yi sakamakon mamakon ruwan saman mutane 3 sun mutu, wasu 9 kuma sun samu raunuka.Labarai masu alaka