Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 13.01.2020

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 13.01.2020.

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 13.01.2020

Alsharq Alawsat: An kai hari da makamai masu linzami kan sansanonin Amurka dake arewacin Bagadaza.
Al-Raya Al-Qatariya: A zanga-zangar Iraki… Dubunnan mutane ne suka jikkata a artabu da 'yan sanda.

Alsharq Alawsat: Iran ta musanta rahotanni game da gaskiyar fadowar jirgin saman Yukren.

 

Le Monde: Shiga tsakanin Turkiyya da Rasha ya kawo tsagaita wuta a Tripoli, babban birnin Libiya.

Faransa 24: Game da sauya dokar 'yan fansho, Firaministan Faransa, Edouard Philippe ya ce abubuwa zasu cigaba da tfiyar har karshe lamarin.

Liberation: Bayanin hukumomi game da jirgin saman Boeing da ya fado a Iran ya haifar da fushi.

 

La Vanguardia: Turkiyya  ta ayyana tsagaita wuta a Libiya da Idlib a matsayin "diflomasiyyar zaman lafiya" da take da ita.

El País: Gwamnatin Spaniya tana son cimma yarjejeniya da ƙungiyoyin kwadago da ma'aikata a matsayin saƙon farko kan mafi ƙarancin albashi.

La Tercera: Real Madrid ta doke Atletico Madrid a wasan bugun daga kai sai maitsaron gida na wasan karshe inda ta lashe gasar Super Cup ta Spaniya.

 

Jaridar Rasha "Kommersant": Ibtila'in fadowar jirgi a Tehran: Yukren za ta nemi diyya.

Jaridar Izvestiya: Ministan Harkokin Wajen Austriya ya ce bai yadda da takunkumin kan bututun man "Nord Stream-2" ba.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha TASS: Amurka da Turkiyya sun tattauna kan hanyoyin karfafa rawar da NATO ke takawa a Gabas ta Tsakiya.

 

Deutsche Welle: Shugaban Turkiyya, Erdoğan ya karbi bakuncin Charles Michel, Shugaban Majalisar Tarayyar Turai a Istanbul don tattauna batun Libiya.

Die Welt: Trump ya yi alkawarin bayar da goyon baya ga zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran

Tagesschau: Firaministar Australiya ta bada haske don sauya manufofin kasar kan yanayi.


Tag: Labarai

Labarai masu alaka