Iran ta kame jakadan Birtaniya a kasarta

An sanar da kame jakadan Ingila a Iran Rob Macaire a taron zaman makokin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar faduwar jirgi mallakar kanfanin jirgin saman Yukiren a Tahran

Iran ta kame jakadan Birtaniya a kasarta

An sanar da kame jakadan Ingila a Iran Rob Macaire a taron zaman makokin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar faduwar jirgi mallakar kanfanin jirgin saman Yukiren a Tahran.

A taron da aka gudanar a kofar jami'ar Emir Kebir  an tabbatar da cewa an samu tada kayar baya inda wasu suka dinga rera taken kalubalantar hukumar kasar lamarin da aka zargi jakadan Ingila a Iran da tursasa mutane a kasar.

A sabili da haka ne anka kame jakadan Ingila a Iran bayan an awanni kuma anka sake shi.

Ministan harkokin wajen Birtaniya  Dominic Raab, ya bayyana cewa "Kame jakadanmu a Iran ba tare da wata dalili ne ba tare da wani bayani ba lamari ne da ya sabawa dokar kasa da kasa"

Raab ya kara da cewa Iran tana daf da wuce gona da iri.

Ko dai ta kasance kasa wacce zata bi hanyar siyasa da diflomasi ta kwantar da dukkanin tashin hankali ko kuma ta kasance wacce zata ci gaba da fuskantar kalubalen siyasa da tattalin arziki da suka hada da takunkumi.

Amurka ma ta yi korafi akan lamarin.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Morgan Ortagus, ya bayyana cewa, Sanadiyar sabawa hakkin dan adam da Iran ta yi muna kira ga Birtaniya da ta nemi Iran ta bata hankuri ta kuma kira ga Iran da ta mutunta dukkanin ma'aikatar diflomasiyar ta.

 Labarai masu alaka