Wani karamin jirgi ya yi hatsari a Amurka

Hatsarin wani karamin jirgi a yankin Lafayette dake jihar Louisiana a Amurka mutane biyar sun rasa rayukansu inda wani daya ya raunana

Wani karamin jirgi ya yi hatsari a Amurka

Hatsarin wani karamin jirgi a yankin Lafayette dake jihar Louisiana a Amurka mutane biyar sun rasa rayukansu inda wani daya ya raunana.

Dangane da bayanan da aka karbo karamin jirgin ya tashi ne daga filin tashi da saukar jiragen saman Lafayette inda ya fado akan wani ginar ma'aikatar wasiku  daga nisan kilomita 1.6 .

Hukumar yan sandan Lafayette ta sanar da cewa uku daga cikin shida mutanen dake jirgin matuka ne.

Wadanda lamarin ya faru akan idonsu sun bayyana cewa jirgin ya yi yunkurin saukar gaggawa jin kadan bayan tashinsa gabanin ya fadi.

Kawo yanzu dai baa bayyana dalilin hatsarin jurgin ba.

 Labarai masu alaka