'Yan Houthi sun sake mutane 23 da suka kama

'Yan Kungiyar Houthi sun bayyana cewa sun saki mutane 23 da suka kama inda suka ce mutanen na San'a babban birnin Yaman.

'Yan Houthi sun sake mutane 23 da suka kama

'Yan Kungiyar Houthi sun bayyana cewa sun saki mutane 23 da suka kama inda suka ce mutanen na San'a babban birnin Yaman. 

Labarin an samo sa ne daga tashar Al-Masira inda aka tabbatar da cewa 'Yan Houthi sun sake mutane 23 wadanda suka kasance suna cikin tawagar sojojin kawancen da Saudiyya ke jagoranta. 

Ila yanzu dai babu bayani game da al'amarin daga bakin gwamnatin Yaman ko kuma sojojin kawancen.

A gefe guda gwamnatin Yaman ta sha bayyana cewa 'Yan Houthi sun kama 'yan jarida, lauyoyi da 'yan siyasa da dama inda 'Yan Houthi suka ki amince wa da tukumar ila yau. 

 Labarai masu alaka