Erdogan ya ce an samu cigaba matuka a tattalin arzikin Turkiyya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ba ta taba kusantan burinta ba kamar yanzu.

Erdogan ya ce an samu cigaba matuka a tattalin arzikin Turkiyya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ba ta taba kusantan burinta ba kamar yanzu.

Shugaban Kasar ya yi jawabi ne a wani babban taro da aka shirya a birnin Istanbul inda ya jaddada cewa suna nan akan burinsu na mayarda darajar kasuwanci da Turkiyya ke yi da kasashen waje Dala biliyan 500.

Shugaban ya ce kasuwar hannayen jari na daya daga cikin ababen dake nuna cigaban da ake samu a tattalin arzikin Turkiyya. 

Haka zalika ya ce a mako mai zuwa za a fara bada kwangila game da manyan ayyukan da za a gudanar a kasar. 

A karshe ya tunatar da cewa Turkiyya ta yi sabin yarjejeniyoyi guda 17 da kasar Malesiya inda ya ce cigaban da aka samu na da matukar mahimmanci a cikin gida da waje. 

 Labarai masu alaka