Sojoji da 'yan tawayen Houthi sun fafata rikici a Hudayde

Sojojin gwamnatin Yaman da 'yan tawayen Houthi sun fafata kazamin rikici a yankin Hudeyde da aka amince kan yarjejeniyar tsagaita wuta a cikinsa.

Sanarwar da Dakarun Amalika mai alaka da gwamnati ta fitar ta ce an mayar da martani kan harin mayakan Houthi a yankin Tahita dake kudancin Hudayde.

Sanarwar ta ce an kashe tare da jikkata 'yan tawayen Houthi da yawa sakamakon arangamar.

A gefe guda tashar Al-Misira mallakar 'yan tawayen Houthi ta ce farar hula 1 ya mutu, wani daya ya jikkata sakamakon harin bam da gwamnati ta kai a yankin Tahita.

An bayyana cewar sakamakon hare-haren gidajen fararen hula a gundumar Durayhimi sun kone.Labarai masu alaka