Za a yi babban taro a kasar Iraki domin tattauna wa kan kisan fararen hula

Mataimakin Shugaban Majalisar Iraki Hasan al-Kaabi da jami'an kwamitin majalisa sun yi kiran cewa za a yi babban taron a majalisa inda za a tattauna game da tsananin karfi da aka yi anfani da shi akan masu zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Baghdad.

Al-kaabi ya ce aikin jami'an tsaro shi ne samar da tsaro a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar yaki da cin hanci da rashawa. 

Kamar haka ne dai kwamitin majalissa ya yi rubucaccen bayani inda ya ce yana gayyatar manyan jami'an gwamnati da su halarci babban taron da za a yi a majalisar kasar a ranar Litinin inda ya ce za a tattauna game da "kisan dangin karshe" da aka yi a birnin Hillani.

Kimanin mutane 460 ne suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar da aka fara a ranar 1 ga watan Oktoba inda zanga-zangar ta sa Firaministan kasar ya yi murabus. 

 Labarai masu alaka