Shugaban Hamas zai kai ziyara a wasu kasashe

Shugaban gudanarwa ta kungiyar Hamas Ismail Heniyye zai fita rangadi a kasa da kasa da suka hada har da Turkiyya

Shugaban Hamas zai kai ziyara a wasu kasashe

Shugaban gudanarwa ta kungiyar Hamas Ismail Heniyye zai fita rangadi a kasa da kasa da suka hada har da Turkiyya.

Dangane da bayanan da aka karbo daga Falasdin bayan zabar Heniyye da aka yi a shekarar 2017 zai fita rangadi zuwa kasashen Katar, Turkiyya da Malaeysia karo na farko.

Tun bayan zaben Heniyye a matsayin shugaban Hamas sau daya ya taba fita waje a lokacin da ya ziyarci Misira kawai.

Heniyye zai yi amfani da filin tshi da saukar jiragen saman Alkahira dake Misira wanda shi ne Falasdinwa mazauna Zirrin Gaza ke amfani dashi kachal domin ziyartar kasashen waje.

An kuma bayyana cewa ziyarar ta Heniyye zata iya daukar watanni.

 Labarai masu alaka