"Ba zamu yarda Amurka ta gina asibiti a Gaza ba"

Shugaban kasar Falasdin Mahmud Abbas ya bayyana cewa ba zasu taba yarda da Amurka ta gina asibitin Sahara a Gaza ba

"Ba zamu yarda Amurka ta gina asibiti a Gaza ba"

Shugaban kasar Falasdin Mahmud Abbas ya bayyana cewa ba zasu taba yarda da Amurka ta gina asibitin Sahara a Gaza ba.

Abbas ya bayyana hakan ne a taron kolin Kungiyar Kare Falasdin da aka gudanar a Ramallah.

Ya kara da cewa, "Wannan tamkar sabawa yarjejeniyar da aka yi shekara da shekaru ne"

Abbas, ya yi kuma sharhi akan yunkurin samar da gurin zama ga Isra'ila ba bisa ka'ida ba a garin  El-Halil, inda ya ce,

"Wannan ba abu ne da za'a yi shiru akai ba, idan har aka gudanar da wannan yunkurin, zai soke dukkanin yarjejeniyar dake tsakaninmu da Amurka da Isra'ila.

Amurka na bukatar gina asibitin Sahara a arewacin Gaza dake da iyaka da Isra'ila.

Ana bukatar ayyanar da wannan aikin na gina asibitin ta hannun wata kungiya mai zaman kanata mai suna 'Friend Ships' daga Amurka tare da yin yarjejeniya tsakanin Kungiyar Kare Gaza da Misisra da Isra'ila.

Sai dai Ramallah na kalubalantar wannan lamarin da kungiyoyin kare Gaza dake Gaza da Hamas ke nazari akan lamarin.

 Labarai masu alaka