An kai hari gidan shugaban Sadr a Iraki

Wani jirgi marar matuki da ba a san daga ina yake ba ya yi luguden wuta a kan gidan Shugaban Kungiyar Sadr dake birnin Najaf a kasar Iraki.

An kai hari gidan shugaban Sadr a Iraki

Wani jirgi marar matuki da ba a san daga ina yake ba ya yi luguden wuta a kan gidan Shugaban Kungiyar Sadr dake birnin Najaf a kasar Iraki. 

Wani kusa a kungiyar mai suna Salih al-Iraki ya yi jawabi ta shafinsa na zumunta inda ya tabbatar da cewa an kai hari gidan babban shugaban dake yankin al-Hanana. 

A gefe guda a jiya ma dai an kai wa 'yan kungiyar hari a zanga-zangar da aka gudanar a biranen Najaf da Baghdad.

Bayanin bai yi magana game da rasuwar mutane sakamakon harin jirgi marar matuki ba.

Tag: hari , Iraki

Labarai masu alaka