Amurka ta tura wakilinta zuwa Iraki

Rahotanni daga Ofishin Harkokin Wajen Amurka sun nuna cewa wakilin Amurka na musamman a harkokin Siriya James Jefferey zai yi ganawar diflomasiyya a kasar Iraki.

Amurka ta tura wakilinta zuwa Iraki

Rahotanni daga Ofishin Harkokin Wajen Amurka sun nuna cewa wakilin Amurka na musamman a harkokin Siriya James Jefferey zai yi ganawar diflomasiyya a kasar Iraki.

Bayanin ya nuna cewa Jeffrey zai gana game gudanar da ayyuka a kasar Siriya da Iraki wajen ganin cewa galabar da aka ci akan 'Yan DEASH ta wanzu. 

Bayanin ya cigaba da cewa Jeffrey zai wuce Kebabben Yankin Kurdawa domin gana wa da gwamnatin yankin inda aka ce, "ziyarar da wakilin ke gudanar wa yana yin ta ne ba dan komai ba, sai dan Amurka ta tallafa wajen samar da Iraki mai wanzuwa da kuma 'yancin kai". 

 Labarai masu alaka