An kai wa sojojin Amurka hari a Iraki

A jihar Salahaddin dake Iraki an kai hari da makami mai linzami kan sansanin sojin Amurka.

An kai wa sojojin Amurka hari a Iraki

A jihar Salahaddin dake Iraki an kai hari da makami mai linzami kan sansanin sojin Amurka.

Sashen yada labarai na rundunar sojin Iraki ya bayyana cewar an kai harin kan sansanin balad da makamai masu linzami guda 2 samfurin Katyusha.

Sanarwar ta ce ba a samu asarar rai ko daya ba sakamakon harin sannan ba a bayyana su waye suka kai wa sansanin hari ba.

Kwanaki 2 da suka gabata an kai hari sansanin Aynul Asad na sojin Amurka dakelardin Anbar din Iraki.Labarai masu alaka