Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 3.12.2019

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 3.12.2019.

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 3.12.2019

Al-Raya Al-Qatariya: Yarjejeniyar Turkiyya da Libya ta kasance doka. 

VATAN: A Siriya sojojin Rasha 3 ne suka jikkata sakamakon fashewar bam da aka binne a kasa.

Alsharq Alawsat: Zanga-zangar da ta gabata a Iran ita ce zanga-zanga da aka fi zubar da jini a kasar a cikin shekaru 40.

 

El Pais: Sarkin Spaniya na 6 Felipe ya ce "Babu iyaka da za ta bada kariya daga dumamar yanayi".

El Mundo: Gwamnatin Sanchez ta nemi yuro biliyan 35 a cikin watanni biyu don cimma burin ta.

Clarin: Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya yi magana game da harajin fari da bakin karfe. Ya ce kuma muna fata Trump ba zai hukunta mu ba.

 

Le Temps: Washington tana son ta ɗora haraji mai yawa kan kayayyakin Faransa.

Le Parisien: Taron 5 ga watan Disamba game da sake fasalin fansho, taron NATO ... (Fadar Shugaban Faransa) Mako guda tare da manyan hadurra ga Fadar Elysée.

Le Monde: A zabukan kananan hukumomi a Paris, ƙazanta kan tituna su ne tushen yaƙin neman zabe.

 

DW: Erdogan ya zauna a tebur tare da shugabannin Turai.

Spiegel Online: Muna matsawa zuwa wani wuri da ba za'a iya canzawa ba a sauyin yanayi.

Focus Online: Batun sake neman mafaka mai maimaituwa. Akwai mutane dubu 4 da dari 9 da 16 da ke neman mafaka a Jamus a karo na uku. Yawan masu neman mafaka a karo na biyar ya kai aƙalla 294.

 

TASS: Shugaban kasar Turkiyya, Erdogan ya ce ba makawa sai an sabunta ayukan NATO.

RIA Novosti: Turkiyya na yin nazara game da shawarar Rasha kan samfurin Su-35. 

Lenta.ru: Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu kan wata doka da ta hana sayar da wayoyi da kwamfutoci ba tare da shigar da manhajan Rasha ba.Labarai masu alaka