Sojojin Turkiyya-Rasha sun gudanar da sintiri na 12 a Siriya
An kammala aikin sintiri na 12 da sojojin Turkiyya da na Rasha ke gudanarwa a yankin Kamisli-Derik dake gabashin Firat

An kammala aikin sintiri na 12 da sojojin Turkiyya da na Rasha ke gudanarwa a yankin Kamisli-Derik dake gabashin Firat.
Dangane da bayanin da Ma’aikatar Tsaro ta yi, an kammala sintirin sojojin a cikin yankin Kamisli-Derik kamar yadda aka tsara.
A kone bangaren masu sintirin sun kasance da motocin yaki hurhudu inda a jumlace aka yi amfani da motocin yaki takwas da wasu jirage marasa matuka.
An gudanar da sintiri a kan hanya mai nisan kilomita 7 da kilomita 69.