Yawan mutanen da suka rasu a girgizar kasar Albeniya ya karu

Yawan mutanen da suka rasu a girgizar kasar Albeniya mai girman Richter 6.3 ya karu inda adadin ya kai 50.

Yawan mutanen da suka rasu a girgizar kasar Albeniya ya karu

Yawan mutanen da suka rasu a girgizar kasar Albeniya mai girman Richter 6.3 ya karu inda adadin ya kai 50.

Bayanin ya zo ne daga bakin Shugaban Kasar Edi Rama inda ya ce an kamalla ayyukan neman wadanda suka bata sakamakon girigizar kasar inda ya ce ila yau mutane 50 ne suka rasa rayukansu. 

Haka zalika Ofishin Gudanar Ayyukan Kiwon Lafiya ya bayyana cewa mutane 913 ne suka jikkata a ranar 26 ga watan Nuwamba da aka yi girgizar kasar. 

Kasashe kamarsu Turkiyya, Masedoniya, Kosobo da Girka sun tallafa da kwararru wajen gudanar da ayyukan neman wadanda suka bata sakamakon girgizar kasar.

Gwamnatin Turkiyya ta bayyana cewa Turkish Crecent ta tura taimako Albeniya bayan an yi girgizar kasar. 

Bayan girgizar kasar mai girman Richter 6.3 an kara yin wasu kanana kusan sau dari inda girman su ya kai Ma'aunar Richter 5.1. 

 Labarai masu alaka