Tarayyar Afirka ta gargadi Ingila

Tarayyar Afirka ta ta gardadi Ingila da cewa ta yi maza ta kawo karshen mulkin mallakan da take yi a tsibiran Chagos wadanda ke karkashin mallakar Jamhuriyar Mauritius.

Tarayyar Afirka ta gargadi Ingila

Tarayyar Afirka ta ta gardadi Ingila da cewa ta yi maza ta kawo karshen mulkin mallakan da take yi a tsibiran Chagos wadanda ke karkashin mallakar Jamhuriyar Mauritius.

Shugaban kwamitin gudanar da ayyukan Tarayyar Afirka Musa Faki Muhammed ya wallafa wani rubuceccen bayani inda ya ce, Ingila ta take dukkan dokikin Majalisar Dinkin Duniya yayinda take gudanar da mulkin mallaka a tsibiran Chagos dake Tekun Indiya inda ya ce hakan yana matukar bakan ta musu rai.

Mista Muhammed ya cigaba da cewa za su cigaba da marawa Mauritius dama domin kasar ta samu 'yancin kanta inda ya tunatar da cewa wa'adin da aka ba wa Ingila na fita daga Mauritius ya cika a yau ranar 22 ga watan Nuwamba. 

A watan Fabrairun da ya gabata ne dai Kotun Duniya ta shawarci Ingila da ta fita daga kasar inda Majalisar Dinkin Duniya ta tilas wa Ingila fita a ranar 22 ga watan Mayu inda ta ce ta ba ta watanni 6 ta kawo karshen mulkin mallakar. Labarai masu alaka