Mummunar girgizar kasa ta afku a Iran

Mutane 6 ne suka mutu, sama da 300 suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 5.9 a jihar Azerbaijan ta gabas da ke arewacin Iran.

Mummunar girgizar kasa ta afku a Iran

Mutane 6 ne suka mutu, sama da 300 suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 5.9 a jihar Azerbaijan ta gabas da ke arewacin Iran.

A cikin wata sanarwa, Cibiyar Nazari kan girgizar kasa ta Jami'ar Tehran, ta ce, a garin Terk na tsakiyar jihar Azerbaijan ta Gabas ne girgizar kasa mai karfin awo 5.9 ta apku da misalin karfe 02.17.

An bayyana ce wa girgizar ƙasa ta faru a zurfin kilomita 8.

Gidan talabijin din kasar ta Iran ta bayar da rahoton cewa, mutane 6 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar, mutane sama da 300 sun ji rauni.

An ji girgizar kasar a jihohin Gilan, Zanjan, Ardabil da Kazvin kuma ta haifar da asara.Labarai masu alaka