Girgizar kasa ta afku a Indonesia

Girgizar kasa mai karfin awo 5.4 ta afku a jihar Sulawesi ta arewacin Indonesia.

Girgizar kasa ta afku a Indonesia

Girgizar kasa mai karfin awo 5.4 ta afku a jihar Sulawesi ta arewacin Indonesia. 

Hukumar Kula da Yanayi da kasa ta sanar da cewa girgizar ta afku da zurfin kilomita 84 tsakiyar yankin Melonguane, Talaud mai nisan kilomita 184 arewa maso yamma da Tsibirain Talaud.

Rahotannin farko sun ce babu wanda ya mutu ko jikkata sakamakon girgizar kasan.

Ba a ba da sanawar yiwuwar ƙara tsunami ba bayan girgizar.Labarai masu alaka