Dusar kankara ta yi ajalin mutane da dama a yankin Jammu Kashmir na Indiya

Sakamakon zubar dusar kankara da yawa a yankin Jammu Kashmir na kasar Indiya mutane 6 da suka hada da sojoji 2 sun rasa rayukansu.

Labaran da jaridun Indiya suka fitar na cewa a yankin Kupvara an samu zubar dusar kankarar wanda ya janyo raguwar karfin ganin masu ababan hawa. Wannan lamari ya janyo hantsilawar motar sojoji inda jami'ai suka mutu.

A wannan yankin dai tarin dusar kankara ta danne wata mota ida was mutane 2 suka mutu.

A yankunan jihar daban-daban mutane 6 aka tabbatar sun mutu sakamakon ibtila'in.

Hanyoyi da dama sun lalace inda bishiyu da yawa suka karye. An soke tashin jiragen sama 11.Labarai masu alaka