An kakkabo jirgi mara matuki a Siriya

Rundunar Siriya ta kakkabo wani jirgi mara matuki a yankin garin Ayn Isa dake arewacin Siriya

An kakkabo jirgi mara matuki a Siriya

Rundunar Siriya ta kakkabo wani jirgi mara matuki a yankin garin Ayn Isa dake arewacin Siriya.

Dakarun Siriya mai taken SMO na ci gaba da gudanar da bincike a yankunan da aka ayyanar da farmakin tafkin zaman lafiya domin samar da tsaro. A yayinda suke gudanar da wannan aikin ne a yankin M4 suka  lura da wani jirgi mara matuki mallakar kungiyar ta'addar YPG/PKK kuma suka harbo shi.

Kungiyar taaddar YPG/PKK na ci gaba da kai hare hare a yankunan Tel Abyad da Tasulayn da aka ayyanar da farmakin tafkin zaman lafiya duk da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Turkiyya da Amurka na su fice daga yankunan.

Suna yawan amfani da jirage marasa matuka domin kai harin ta'addanci.

 

 

 

 Labarai masu alaka