Kungiyar Houthi ta kai hari a sansanin sojojin Saudiyya

An bayyana cewa kungiyar Houthi dake Yaman sun kai hari a wani sansanin sojojin Saudiyya dake garin Nejran a kudu maso yammacin kasar da makami mai linzami.

Mai magana da yawun kungiyar Houthin da Iran ke goyawa baya Yahya Seri ya yada wata sanarwa a shafukansa nas adar da zumunta da cewa sun kai hari da makami mai linzami sanfarin "Bedir F"  a sansanin sojojin Saudiyya dake garin Nejran dake kudu maso yammacin kasar.

Seri ya bayyana cewar harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama an kai shi ne bayan samun labaren sirrin da aka samu cewa sojojin da Saudiyya ke jagoranta na shirin kaiwa kungiyar Houthi hari.

Kawo yanzu dai Saudiyya da dakarun da take goyawa baya a Yaman basu ce ko uffan ba akan lamarin.

 Labarai masu alaka