An kashe 'yan kungiyar Houthi 20 a Yaman

An bayyana cewar a wata arangama da aka kwasa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan kungiyar Houthi a garin Marib dake gabashin Yaman an kashe yan kungiyar Houthin 20.

Kamar yadda kafar yada labaran 26sepnews ta gwamnati ta rawaito a yayinda 'yan kungiyar Houthi ke kokarin mamaye yankin da dakarun gwamnati suke a garin Sirvah dake karkashin Marib rikici ya barke kuma anyi nasarar kashe 'yan kungiyar 20 inda wasunsu kuma suka raunana.

Ba'a dai bayyana ko an samu hasarar rayuka daga yankin jami'an gwamnatin ba.

Sanarwar ta kara da cewa dakarun da Saudiyya ke jagoranta sun kai hari ta sama a yankin da 'ya'yan kungiyar Houthi ke zaune. A harin an lalata kayan yakin 'yan kungiyar amma ba'a bayyana ko su nawa aka kashe ko raunana ba.

Kungiyar Houthi dai bata fitar da wata sanarwa ba akan lamarin.

Tun daga watan Satumbar 2014 kawo yanzu babban birnin kasar Sana da wasu yankunan kasar ke hannun kungiyar Houthi.

Dakarun da Saudiyya ke jagoranta kuwa sun fara kaiwa kungiyar hari ne a watan Maris din shekarar 2015.

 Labarai masu alaka