An harbe babban Malamin Sunnah dan kasar Iran

Sakatare Janar na Iran Ahlussan Ibrahim Safizade ya rasa ransa a asibitin da aka kwantar da shi bayan harbin sa da bindiga da aka yi a garin Herat na kasar Afganistan a ranar Juma'ar da ta gabata.

Bayanan da majiyoyin yankin suka fitar na cewa, a ranar Juma'ar makon da ya gabata ne wasu da ba a san ko su waye ba ne suka harbin malamin wanda ya rasa ransa a asibitin da yake jiyya.

Sanarwar da Kungiyar Iran Ahlussunah dake adawa da Iran ta fitar ta bayyana cewar Iran na da alaka da kashe Malamin.

Kusan shekaru 20 da suka gabata Ibrahim Safizade ya yi hijira daga kasarsa zuwa Afganistan sakamakon matsin lamba da yake fuskanta.Labarai masu alaka