Yaki ba zai barke tsakanin Iran da Amurka ba

Shugaban ofishin harkokin wajen Iran Muhammed Javad Zarif, ya bayyana cewa yanada tabbas kan cewa yaki ba zai barke tsakanin Amurka da Iran ba.

Yaki ba zai barke tsakanin Iran da Amurka ba

Shugaban ofishin harkokin wajen Iran Muhammed Javad Zarif, ya bayyana cewa yanada tabbas kan cewa yaki ba zai barke tsakanin Amurka da Iran ba.

A ziyarar da ya kai kasar Sin ne dair mista Zarif ya yi bayani a tashar labaren Iran mai suna IRNA

Bayan tambayar da aka masa game da yaki tsakanin Amurka da Iran ne dai Zarif ya ce “Ba za a yi yaki tsakanin Iran da Amuraka ba sabida mu dai ba yaki muke so ba, sannan babu wata kasa a yankin da zata ta so ta ga faruwar hakan”.

Zarif ya shaida cewa yana da masaniya kan cewa akwai jama’a da dama zagaye da Trump wadanda ke zugashi domin yaki ya barke tsakanin kasashen biyu.

Bayan wannan bayani Zarif ya kara da cewa, “Trump ya bayyana cewa baya son yaki, mutanen da ke zagaye da shi ne ke iza wutar rigima”.

Gwamnatin Tehran ta ce tanada tabbacin cewa, shugaban harkokin tsaron Amurka John Bolton yana hadin gwiwa da Saudiya, Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa domin su kaiwa Iran hari.

Tashoshin labaren Amurka na nuna cewa Trump ya kasa sasantawa da masu bashi shawara game da matsalar Iran. To sai dai Trump ya ce shi dai bashi da wata matsala ko kadan da mashi ba shi shawara.Labarai masu alaka