A karon farko girgizar kasa ta afku a duniyar Mars

Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta bayyana cewar bayan ajje na'ura auna afkuwar girgizar kasa ta InSight a duniyar Mars ta gano an samu motsawa da karkarwa a duniyar.

Masanan Kimiyya sun fadi cewa, a ranar 6 ga watan Afrilu na'urar InSight ta gano an samu diri da kadawa a Mars kuma wannan ce girgizar kasa ta farko da aka samu a duniyar sama.

Jami'in Cibiyar Bincike Kan Yanayin Kasa ta Paris mai suna Philippe Lognonne ya ce, sun dimauta kan yadda har yanzu ake iya ganin alamun motsawar duniyar ta Mars.

Ya ce "tsawon watanni suna jiran su ga abu makamancin haka.

An bayyana cewar kwararru na ci gaba da aiyukan bincike da nazari kan motsi 3 da aka samu a watannin Maris da Afrilu.Labarai masu alaka