An kone Kur'ani a Danmak

Dubban 'yan Danmak sun mamaye titunan kasarsu da zummar yin Allah wadai da kone Al Kur'ani mai Tsarki da Rasmus Paludan,shugaban jami'yyar siyasa mai makaho tsaurin ra'ayi na Stram Kurs ya yi.

An kone Kur'ani a Danmak

Dubban 'yan Danmak sun mamaye titunan kasarsu da zummar yin Allah wadai da kone Al Kur'ani mai Tsarki da Rasmus Paludan,shugaban jami'yyar siyasa mai makaho tsaurin ra'ayi na Stram Kurs ya yi.

Akalla kungiyoyin fararen hula 24 ne suka hada karfi da karfe da nufin bayyana girmamawarsu ga Tsarkakken littafin na addinin Musulunci da kuma yin tofin Allah tsine kan Rasmus Paludan.

A sahun wadanda suka halarci wannan tattakin akwai kungiyoyin fararen hula na Turkawa,kusoshin hukumar da ke kula da lamurran da suka jibanci Musulunci ta Dandmak (DTDV), Hadakan Musulman Danmak (DİT),Hadakan 'yan demokradiyyar kasa da kasa (UID) da kuma wasu kungiyoyin kwadago na Danmak,wadanda dukanninsu suka taru a bakin kofar cibiyar kafar yada labarai ta Blaagards Plads dauke da wasu allunan da aka rubuta ayayin alkur'ani a kansu,kafin daga bisani su doshi ma'aikatar magajin garin Kopenhag.

A yayin wannan tattakin masu zanga-zangar sun dinka yin kabbara da kuma sukar lamarin Rasmus Paludan,inda bayan sun isa filin Kopenhag suka yi kiran sallah, furta albarkacin bakunsu da kuma watsayewa salim-alim ba tare da wata fitina ta kunno kai ba.

Kungiyoyin Danmak wadanda suka bada nasu tallafin wajen shirya wannan zanga-zangar sun kira da a gaggauta dakatarcda kone tsarkakken litattafai,musamman ma Al Kur'ani mai Tsarki.Saboda hakan ba dadai ba ne.

Don cimma burin da suka gaba, masu zanga-zangar sun dinka bi gida-gida don samun isassun sa-hannu.

Za a dai mika wadannan sa-hannu ga 'yan siyasa don daukar dukannan matakan da suka da dace don magance ire-iren wadannan ma kone manyan litattafai na addinai.


Tag: danmak

Labarai masu alaka