Hare-hare a masallatan Ingila

Yawan masallatan da aka kai wa hari a baya-bayan nan a birnin Birmingham na kasar Burtaniya ,ya haura 5.

Hare-hare a masallatan Ingila

Yawan masallatan da aka kai wa hari a baya-bayan nan a birnin Birmingham na kasar Burtaniya ,ya haura 5.

A wata sanarwar da 'yan sandan Ingila suka fitar a ranar Alhamis din nan da ta gabata,an tabbatar da cewa,an kai wa wasu wuraren ibada 5 na mabiya addinin Islama da ke Ingila,hari.

Tuni kuma, aka fara zurfafa bincike kan masallaci na 5 da aka kai wa irin wannan harin na ta'addanci.

An yada hotunan harin da aka kai a cibiyar Musulunci ta Aston, a shafukan sada zumunta.

Wadanda  suka aikata wannan ta'asar sun yi amfani da gunduma wajen farfasa gilasan tagogin wurin ibadar.
Ministan tsaron gida na kasar Ingila,Sajid Javid ya bayyana a shafinsa na sada zumunta ba Twitter cewa,"Wadannan hare-haren na matukar tayar mana da hankali.Wannan babban abin kunya ne da ya afka wa al'umar Burtaniya".
Wannan mummunan lamarin dai ya kunno kai kusan mako daya tak da afkuwar tagwayen hare-haren ta'addancin da aka kai a wasu masallatan Jumma'a 2 na  kasar Niyuzelan.Abinda ya rutsa da rayukan Musulmai 50.

Kawo yanzu ba a gano maharan na kasar Ingila, ba a kuma bayyana dalilin yasa su aikata wannan danyen aikin.

A wadannan shekaru 3, a kasar Burtaniya,hare-haren da ke nasaba da kyamar Musulmai na ci gaba da ninkuwa,inda a shekarar 2018 aka far wa musulmai da wuraren ibadarsu sau 1200,wanda hakan yayi daidai da karin hare-hare da kashi 26 cikin dari, idan aka yi la'akari da alkalanman shekarar 2017.


Tag: Ingila

Labarai masu alaka